Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.

  2. A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,

  3. Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace,

  4. Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.

  5. Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa,

  6. waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki,

  7. suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe.

  8. Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu.

  9. Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku.

  10. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci

  11. duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

  12. Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari.

  13. Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.

  14. ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala.

  15. Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse,

  16. suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.

  17. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

  18. Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.

  19. Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya.

  20. Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa

  21. Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,

  22. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.

  23. Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”

  24. Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.”

  25. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.