Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.

  2. Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba?

  3. Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa.

  4. Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul.

  5. Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’

  6. “Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.

  7. Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku suna yawo daga arewa zuwa kudu, suna neman maganar Ubangiji, amma ba za su samu ba.

  8. Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce, “Bugi kan ginshiƙan don madogaran ƙofa su girgiza. Saukar da su a kan dukan mutane; waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi. Ba mutum guda da zai tsere, babu wani da zai tsira.

  9. Wahayin Obadiya. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom. Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa, An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa, “Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.”

  10. Maganar Ubangiji ta zo wa Yunana ɗan Amittai cewa,

  11. Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.

  12. “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”

  13. Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

  14. Masu gani za su ji kunya, masu duba kuma za su ji taƙaici. Dukansu za su rufe fuskokinsu gama ba amsa daga Allah.”

  15. Amma game da ni, ina cike da iko ta wurin Ruhun Ubangiji da kuma adalci da ƙarfi, don a sanar da Yaƙub laifofinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa.

  16. Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh.

  17. Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa.

  18. Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka rubuta wannan ru’uya ka bayyana ta a fili a kan alluna don mai shela yă ruga da ita, yă kai.

  19. Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.

  20. Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.

  21. Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.

  22. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.

  23. Sai Haggai, ɗan saƙon Ubangiji, ya ba da wannan saƙo na Ubangiji ga mutane cewa, “Ina tare da ku” in ji Ubangiji.

  24. A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

  25. 7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.