Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yayinda yake magana da ni, barci mai nauyi ya kwashe ni, da nake kwance rubda ciki. Sai ya taɓa ni ya kuma tashe ni tsaye.

  2. Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe.

  3. Rago mai ƙahoni biyu da ka gani, yana a madadin sarakunan Medes da Farisa ne.

  4. Bunsurun kuwa sarkin Girka ne, kuma babban ƙahon da yake tsakanin idanunsa, sarki na farko ne.

  5. Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba.

  6. “Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito.

  7. Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka.

  8. Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.

  9. “Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.”

  10. A shekara ta fari da mulkin Dariyus ɗan Zerzes (wanda yake Bamediye), wanda aka mai da shi sarki a masarautar Babiloniyawa

  11. a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.

  12. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.

  13. Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa,

  14. mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.

  15. Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.

  16. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.

  17. Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.

  18. Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;

  19. ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.

  20. Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.

  21. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.

  22. Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba.

  23. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.

  24. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.

  25. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.