- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone.
Ta gajiyar da dukan ƙoƙari; ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba, kai, ko a wuta ma.
“ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.
“ ‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
“Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye.
Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”
Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni.
Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?”
Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku. ’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi.
Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba.
Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.
Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’
To a yamman da ya wuce kafin mutumin ya iso, hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma buɗe bakina kafin mutumin ya iso wurina da safe. Sai bakina ya buɗu ban kuma yi shiru ba.
Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa.
A shekara ta ashirin da biyar ta zaman bauta, a farkon shekara, a rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha huɗu bayan fāɗuwar birnin Urushalima, a wannan rana ikon Ubangiji ya sauko a kaina ya kuma iza ni.
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin fili na can ciki, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.
A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama.
Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a can, na tambaye shi gaskiya ma’anar waɗannan al’amura. “Don haka sai ya faɗa mini, ya kuma ba ni fassarar waɗannan al’amura.
“Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.”
Yayinda ni, Daniyel, nake duban wahayi ina ƙoƙari in fahimce shi, sai ga wani a gabana wanda ya yi kama da mutum.
Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.”
Da ya zo kusa da inda nake tsaye, na firgita na kuma fāɗi rubda ciki. Ya ce da ni “Ɗan mutum, ka gane da cewa wannan wahayi yana magana ne a kan kwanakin ƙarshe.”