Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophecies Respecting Christ

253 ayoyi · 66 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama idanuna sun ga cetonka,

  2. wanda ka shirya a gaban dukan mutane,

  3. haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”

  4. Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu.

  5. Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,

  6. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

  7. In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”

  8. Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa.

  9. Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”

  10. Amma ya ce, “Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.”

  11. Yesu ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

  12. “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.”

  13. Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.

  14. A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne.

  15. Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

  16. Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,

  17. Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu.

  18. suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”

  19. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.

  20. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.

  21. Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima.

  22. A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi.

  23. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.

  24. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”

  25. Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”