Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Riches

225 ayoyi · 107 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi.

  2. Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.

  3. Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.

  4. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

  5. Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.

  6. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.

  7. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;

  8. domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.

  9. Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.

  10. Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.

  11. Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.

  12. Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba.

  13. Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

  14. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

  15. Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

  16. Akwai wani mutum shi kaɗai; bai shi da ɗa ko ɗan’uwa. Ba shi da hutu daga wahalarsa, duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba. Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala, kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?” Wannan ma ba shi da amfani, harkar baƙin cikin ne kawai!

  17. Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki.

  18. Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.

  19. Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?

  20. Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci.

  21. Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi,

  22. ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa.

  23. Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa.

  24. Wannan ma mugun abu ne, Yadda mutum ya zo, haka zai koma, to, wace riba ce ya ci, da yake ya yi wahalar iska ce kawai?

  25. Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu, da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi.