Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Riches

225 ayoyi · 107 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.

  2. Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

  3. A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.

  4. To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne.

  5. Wata rana Elisha ya tafi Shunem. Akwai wata mai arziki a can wadda ta gayyace shi cin abinci. Sai ya zama duk lokacin da yake wucewa, yakan tsaya a can don cin abinci.

  6. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,

  7. Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.

  8. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.

  9. Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.

  10. Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma.

  11. Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa.

  12. Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki.

  13. Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai.

  14. Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.

  15. “Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro.

  16. ya yi ta taƙama game da ɗumbun wadatarsa, da yawan ’ya’yansa maza, da dukan yadda sarki ya girmama shi, ya kuma ɗaga shi bisan sauran hakimai da shugabanni.

  17. yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.

  18. Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.

  19. Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.

  20. Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.

  21. Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.

  22. Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa,

  23. “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’

  24. in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.

  25. Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.