Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Riches

225 ayoyi · 107 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

  2. Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.

  3. Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.

  4. Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako.

  5. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  6. Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.

  7. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.

  8. Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.

  9. Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?

  10. Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?

  11. Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?

  12. Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku.

  13. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku.

  14. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe.

  15. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.

  16. Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka.

  17. Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba,

  18. A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini,

  19. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?

  20. Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.

  21. Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka.

  22. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan!

  23. Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”

  24. su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai!

  25. Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa.