Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Riches: Increase, by oppression

6 ayoyi · 107 fannoni

Ayoyi game da Increase, by oppression

  1. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

  2. Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su, ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace. Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa, har ku ƙwace masa gādonsa.

  3. Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne.

  4. “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’

  5. Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.

  6. Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.