Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji.

  2. A shekara ta talatin, a wata na huɗu a rana biyar, yayinda nake cikin ’yan zaman bauta kusa da Kogin Kebar, sai sammai suka buɗe na kuwa ga wahayoyin Allah.

  3. maganar Ubangiji ta zo wa Ezekiyel firist, ɗan Buzi, kusa da Kogin Kebar a ƙasar Babiloniyawa. A can hannun Ubangiji yana a kansa.

  4. Duk inda ruhu za shi, su ma can za su, kuma da’irorin za su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin.

  5. Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.”

  6. Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana.

  7. Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’

  8. Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu.

  9. Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye.

  10. Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su.

  11. Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.”

  12. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ji da kyau ka kuma lura da dukan kalmomin da nake maka magana.

  13. Ka tafi yanzu zuwa ga ’yan’uwanka waɗanda suke zaman bauta ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,’ ko ku ji, ko kada ku ji.”

  14. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama, a bayana na ji wata karar babban motsi na cewa, Bari a yabi ɗaukakar Ubangiji a wurin zamansa!

  15. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da ɓacin rai da kuma fushin ruhuna, tare da hannu mai ƙarfi na Ubangiji a bisa na.

  16. Na zo wurin masu zaman bautan da suke zama a Tel Abib kusa da Kogin Kebar, A can kuwa, inda suke zama, na zauna a cikinsu kwana bakwai, ina mamaki.

  17. A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  18. “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni.

  19. In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.

  20. Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta.

  21. “Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.

  22. Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.”

  23. Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.”

  24. Sai Ruhu ya sauko a kaina ya kuma ɗaga ni na tsaya a ƙafafuna. Ya yi mini magana ya ce, “Ka fita, ka rufe kanka a cikin gida.

  25. Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye.