Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ministers

201 ayoyi · 118 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne.

  2. Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.

  3. Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.

  4. Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.

  5. Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi.

  6. Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba,

  7. Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi.

  8. Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara,

  9. Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake, da kuma abin da nake yi.

  10. Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.

  11. A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum

  12. Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni.

  13. Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi.

  14. Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara.

  15. Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi.

  16. Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa.

  17. Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce.

  18. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.

  19. Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.

  20. Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa,

  21. Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙa’idar da muka ba ku.

  22. I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

  23. Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.

  24. Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.

  25. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.