Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ministers: Without deceitfulness

4 ayoyi · 118 fannoni

Ayoyi game da Without deceitfulness

  1. Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.

  2. Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.

  3. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.

  4. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.