Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Providence of God

163 ayoyi · 41 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.

  2. Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.

  3. Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi.

  4. Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.

  5. Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

  6. Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta.

  7. Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane.

  8. Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

  9. Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka.

  10. Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela

  11. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  12. Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

  13. Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

  14. Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba.

  15. Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.

  16. Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

  17. Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;

  18. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.

  19. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.

  20. Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;

  21. suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.

  22. Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.

  23. Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.

  24. Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.

  25. Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.