Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Providence of God

163 ayoyi · 41 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

  2. Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.

  3. Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

  4. Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  5. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.

  6. Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.

  7. Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.

  8. Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

  9. Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.

  10. can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.

  11. Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.

  12. Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.

  13. Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.

  14. Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.

  15. cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  16. Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.

  17. ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.

  18. Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.

  19. Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika.

  20. Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?

  21. Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.

  22. Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.

  23. “Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!

  24. Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.

  25. Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba, ba abin da yake da shi a zuciya ba; manufarsa shi ne yă hallaka, yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.