Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Providence of God: Ruling the elements

9 ayoyi · 41 fannoni

Ayoyi game da Ruling the elements

  1. Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.

  2. Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.

  3. Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.

  4. Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi.

  5. Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.

  6. Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa? Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa? Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka? Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne? Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku, na mai da koguna hamada; kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa suka kuma mutu saboda ƙishi.

  7. Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; yakan sa dukan koguna su kafe. Bashan da Karmel sun yi yaushi tohon Lebanon kuma ya koɗe.

  8. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

  9. (Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”)