Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Providence of God: Preserving the course of nature
Ayoyi game da Preserving the course of nature
“Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.”
ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.
Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.
Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;
suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.
Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.