Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple

365 ayoyi · 72 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi.

  2. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

  3. sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.

  4. Da Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima, sai ya kwashi ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan sarki. Ya kwashe kome da kome, har da garkuwoyin zinariyar da Solomon ya yi.

  5. kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.

  6. Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji.

  7. Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji.

  8. Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba.

  9. Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?”

  10. Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al.

  11. Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji.

  12. Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada.

  13. Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika.

  14. Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa.

  15. Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin.

  16. Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi.

  17. Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo wurinsa, sai ya wahalar da sarki Ahaz maimakon taimakonsa.

  18. Ahaz ya ɗauki waɗansu abubuwa daga haikalin Ubangiji da kuma daga fadan sarki da kuma daga sarakuna, ya ba da su ga sarkin Assuriya, amma wannan bai taimake shi ba.

  19. A wata na farkon a farkon shekarar mulkinsa, ya buɗe ƙofofin haikalin Ubangiji ya gyara su.

  20. Ya kawo firistoci da Lawiyawa, ya tattara su a filin da yake a gefen gabas

  21. ya kuma ce musu, “Ku saurare ni, Lawiyawa! Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake haikalin Ubangiji Allah na kakanninku. Ku fid da ƙazanta daga wuri mai tsarki.

  22. Kakanninku ba su yi aminci ba; suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnmu, suka kuma yashe shi. Suka juya fuskokinsu daga mazaunin Ubangiji suka kuma juya masa baya.

  23. Suka kulle ƙofofin shirayi, suka kuma kashe fitilu. Ba su ƙone turare ko su miƙa hadayun ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra’ila ba.

  24. Saboda haka, fushin Ubangiji ya fāɗo a kan Yahuda da Urushalima; ya mai da su abin tsoro da abin banrazana da kuma abin ba’a, kamar yadda kuke gani da idanunku.

  25. Abin da ya sa ke nan kakanninmu suka fāɗi ta takobi, kuma shi ya sa aka kai ’ya’yanmu maza da ’ya’yanmu mata da matanmu bauta.