Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection

128 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.

  2. Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’

  3. Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

  4. Suka fito da dukan rundunansu da keken yaƙi masu yawan gaske, babbar runduna, yawansu ya yi kamar yashin bakin teku.

  5. Duk sarakunan nan suka haɗa mayaƙansu tare, suka kafa sansani a bakin Ruwayen Meron don su yi yaƙi da Isra’ilawa.

  6. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.”

  7. Sai Yoshuwa da dukan mayaƙan suka auka musu a bakin Ruwayen Meron.

  8. Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa nasara a kan su, suka ci su da yaƙi, suka fafare su har zuwa Sidon Babba, zuwa Misrefot Mayim, har zuwa Kwarin Mizfa a gabas, ba wanda suka bari da rai.

  9. “Amma in kuka juya baya kuka zama abokai ga waɗanda suka ragu suke zama a cikinku a ƙasashen nan, har kuka yi auratayya da su, kuka haɗa kai da su,

  10. ku tabbata cewa Ubangiji Allahnku ba zai kore muku mutanen ƙasashen nan ba, sai ma su zama muku dutsen tuntuɓe da tarko, za su zama bulala a bayanku, ƙayayyuwa a idanunku, har sai kun hallaka daga wannan ƙasa mai kyau wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.

  11. Ubangiji Allahnmu ne da kansa ya fitar da iyayenmu daga Masar, daga ƙasar bauta, ya yi manyan abubuwan al’ajabi, a idanunmu. Ya kiyaye mu cikin dukan hanyar da muka bi, da cikin ƙasashen da muka ratsa;

  12. Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa, zan cece ka in kuma ba da Midiyawa a hannuwanku. Ka bar sauran mutane su tafi kowa zuwa wurinsa.”

  13. Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba.

  14. Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki, amma mugaye za su lalace cikin duhu. “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;

  15. Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  16. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.

  17. Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”

  18. Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”

  19. In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.

  20. sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.

  21. Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

  22. Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

  23. Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.

  24. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.

  25. Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu.