Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection: Hosts

6 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da Hosts

  1. Suka fito da dukan rundunansu da keken yaƙi masu yawan gaske, babbar runduna, yawansu ya yi kamar yashin bakin teku.

  2. Duk sarakunan nan suka haɗa mayaƙansu tare, suka kafa sansani a bakin Ruwayen Meron don su yi yaƙi da Isra’ilawa.

  3. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.”

  4. Sai Yoshuwa da dukan mayaƙan suka auka musu a bakin Ruwayen Meron.

  5. Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa nasara a kan su, suka ci su da yaƙi, suka fafare su har zuwa Sidon Babba, zuwa Misrefot Mayim, har zuwa Kwarin Mizfa a gabas, ba wanda suka bari da rai.

  6. Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.