Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection: All dangers

5 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da All dangers

  1. Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.

  2. Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

  3. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

  4. ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

  5. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.