Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection: The poor
Ayoyi game da The poor
Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu.
Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.
Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.