Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection: Idols

4 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da Idols

  1. Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki,

  2. allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu? Ku sa su tashi su taimake ku mana! Bari su ba ku mafaka!

  3. “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.

  4. Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi; sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya. Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba. Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa; ba zai iya cetonsa daga wahala ba.