Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection: Calamities
Ayoyi game da Calamities
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.
Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.