Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Protection

128 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.

  2. Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce, Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.

  4. Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.

  5. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.

  6. Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.

  7. Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.

  8. gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.

  9. ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.

  10. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

  11. Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.

  12. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.

  13. Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.

  14. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  15. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.

  16. Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.

  17. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.

  18. Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.

  19. Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce.

  20. Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.

  21. Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

  22. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

  23. ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

  24. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.

  25. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;