Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests

407 ayoyi · 86 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In ya rasa gashin goshinsa yana kuma da sanƙo a goshinsa, shi tsarkakakke ne.

  2. Amma in yana da miki ja-ja da ya yi fari a sanƙonsa ko a goshinsa, cuta mai yaɗuwa ce take fasuwa a kai ko a goshin.

  3. Sai firist ya bincike shi, in kuma kumburarren miki a kansa ko goshinsa ja-ja da fari-fari kamar cutar fatar jiki mai yaɗuwa ne,

  4. mutumin ya kamu da cutar kuma marar tsarki ne. Firist ɗin zai furta mutumin marar tsarki saboda mikin da yake a kansa.

  5. “Mutum mai wannan cuta mai yaɗuwa dole yă sa yagaggun riguna, yă kuma bar gashin kansa ba gyara, yă rufe sashe ƙasa na fuskarsa, sa’an nan yă riga cewa, ‘Marar tsarki! Marar tsarki!’

  6. Muddin yana da cutar zai ci gaba da kasance marar tsarki. Dole yă yi zama shi kaɗai; dole yă yi zama waje da sansani.

  7. “In akwai cutar fatar jiki a riguna, duk wani rigar ulu ko na lilin,

  8. duk wani kayan zare, ko saƙa na lilin, ko ulu, duk wani kayan fata, ko wanda aka yi da fata,

  9. in kuma cutar a cikin rigar, ko fatar, ko kayan saƙan kore-kore ne, ko ja-ja, to, cutar fatar jiki da ake samu a riguna ce mai yaɗuwa, kuma dole a nuna wa firist.

  10. Firist ɗin zai bincike cutar fatar jikin da take a rigar, yă kuma kaɗaice kayan da abin ya shafe shi kwana bakwai.

  11. A rana ta bakwai ɗin zai bincike shi, in cutar rigar ta yaɗu, ko a tariyar zaren, ko a wadarin, ko a fatar, ko kuwa a duk abin da ake amfani da shi, to wannan muguwar cutar riga ce; kayan marar tsarki ne.

  12. Dole yă ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko kayan da aka saƙa na ulu ko lilin, ko kuwa na kaya da aka yi da fatar, wanda cutar ta fāɗa wa, domin cutar rigar muguwa ce, dole a ƙone kayan.

  13. “Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, cutar rigar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zare, ko a kayan da aka saƙa, ko a kayan da aka yi da fata ba,

  14. zai umarta cewa a wanke kayan da cutar ta shafa. Sa’an nan zai kaɗaice shi na waɗansu kwana bakwai.

  15. Bayan an wanke kayan da cutar ta shafa, firist zai bincike shi, in kuwa cutar rigar ba tă canja yadda take ba, ko da yake ba tă yaɗu ba, marar tsarki ce.

  16. In sa’ad da firist ya bincike shi, cutar rigar ta bushe bayan da aka wanke kayan, sai yă yage sashen da cutar ta shafa na rigar, ko fatar, ko tariyar zaren, ko kuwa na kayan da aka saƙa.

  17. Amma in ya sāke bayyana a rigar, ko a tariyar zaren, ko a kayan da aka saƙa, ko a kayan da aka yi da fatar, to, yana yaɗuwa ke nan, kuma dole a ƙone duk abin da yake da cutar rigar da wuta.

  18. Rigar, ko tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk kayan da aka yi da fatar da aka wanke, aka kuma fid da cutar rigar, dole a sāke wanke shi, zai kuwa zama tsarkakakke.”

  19. Waɗannan su ne ƙa’idodi game da cutar fatar jiki na rigar ulu, ko rigar lilin, tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk wani abin da aka yi da fata, don furta su tsarkakakke, ko kuwa marar tsarki.

  20. “Sa’ad da kuka shiga ƙasar Kan’ana, wadda nake ba ku kamar gādonku, na kuma sa yaɗuwa cutar fatar jiki a riga a cikin gida a wannan ƙasa,

  21. dole maigidan ya tafi ya faɗa wa firist ya ce, ‘Na ga wani abu da ya yi kamar cutar fatar jikin da take a riga a cikin gidana.’

  22. Firist zai umarci a fitar da kome a gidan kafin ya shiga ya bincike cutar fatar jiki da take a rigar, saboda babu abin da yake gidan da za a furta marar tsarki ne. Bayan haka firist zai shiga ya dudduba gidan.

  23. Zai bincike cutar fatar jiki da take a riga a bangaye, in kuma yana da tabon kore-kore ko ja-ja da suka bayyana da suka yi zurfi fiye da saman bangon,

  24. firist ɗin zai fita a bakin ƙofar gidan ya rufe ta na kwana bakwai.

  25. A rana ta bakwai ɗin firist zai dawo don yă dudduba gidan. In cutar fatar jiki da take a riga ta yaɗu a bangayen,