Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests: Thirteen of the Levitical cities given to, for residence

12 ayoyi · 86 fannoni

Ayoyi game da Thirteen of the Levitical cities given to, for residence

  1. A filayen Mowab, wajen Urdun, ɗaura da Yeriko, Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,

  2. “Ka umarci Isra’ilawa su ba wa Lawiyawa garuruwan da za su zauna a ciki daga cikin gādon da Isra’ilawa za su mallaka. A kuma ba su wurin kiwo kewaye da garuruwan.

  3. Sa’an nan za su kasance da garuruwan da za su zauna, su sami fili, da kuma za su yi kiwon garkensu na shanu da tumaki da kuma sauran dabbobinsu.

  4. “Wuraren kiwo a kewayen garuruwan da za a ba wa Lawiyawa, girmansu zai zama mai fāɗin kamu dubu ɗaya daga katangar garin.

  5. A bayan garin, ka auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu wajen kudu, da kuma kamu dubu uku wajen arewa, a bar garin a tsakiya. Za su kasance da wannan a matsayin wurin kiwo na garuruwan.

  6. “A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida daga cikin garuruwan za su zama biranen mafaka, inda wanda ya kashe mutum zai gudu yă je. Ban da wannan, a ba su waɗansu garuruwa arba’in da biyu.

  7. Duka-duka dai a ba Lawiyawa garuruwa arba’in da takwas, tare da wuraren kiwonsu.

  8. Garuruwan da za ku ba wa Lawiyawa daga ƙasar da Isra’ilawa suka mallaka, za a ba da su bisa girman gādon kowace kabila. Ka karɓi garuruwa masu yawa daga kabilar da take da garuruwa masu yawa, amma kaɗan daga kabilar da ba ta da garuruwa masu yawa.”

  9. Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,

  10. Hilen, Debir,

  11. Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.

  12. Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.