Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests: Show-bread after its removal

5 ayoyi · 86 fannoni

Ayoyi game da Show-bread after its removal

  1. Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.”

  2. Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”

  3. Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!”

  4. Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.

  5. Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.