Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests: Partaking of the sacrifices of consecration
Ayoyi game da Partaking of the sacrifices of consecration
“Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.
A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon.
Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.
Sai Musa ya ce wa Haruna da ’ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar Tentin Sujada, ku kuma ci shi a can tare da burodi daga kwandon naɗi, yadda na umarta, cewa, ‘Haruna da ’ya’yansa maza za su ci shi.’
Sa’an nan ku ƙone sauran naman da kuma burodin.