Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests: Lighting and trimming the lamps of the sanctuary

4 ayoyi · 86 fannoni

Ayoyi game da Lighting and trimming the lamps of the sanctuary

  1. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai, tatacce daga zaitun domin fitilu, saboda fitilun su yi ta ci a koyaushe.

  2. A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.

  3. Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa.

  4. Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.