Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests: Tenth of the tithes paid to the Levites

5 ayoyi · 86 fannoni

Ayoyi game da Tenth of the tithes paid to the Levites

  1. “Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji.

  2. Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji.

  3. “Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma.

  4. Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali.

  5. Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne.