Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests: Placing in their hands the wave-offering

6 ayoyi · 86 fannoni

Ayoyi game da Placing in their hands the wave-offering

  1. “Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)

  2. Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai.

  3. Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da ’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.

  4. Ya ɗibi kitsen, da wutsiya mai kitse, da kuma dukan kitsen da ke kewaye da kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, ƙodoji biyu da kitsensu da kuma cinya ta dama.

  5. Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama.

  6. Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da ’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.