Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests

407 ayoyi · 86 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A ce sabon mikin ya canja ya juya fari, dole yă je wurin firist.

  2. Firist zai bincike shi, in kuma mikin ya juya ya zama fari, firist zai furta mai cutar tsarkakakke; to, zai zama tsarkakakke.

  3. “Sa’ad da wani yana da kumburi a fatar jikinsa ya kuma warke,

  4. kuma a inda ƙurjin yake, wani farin kumburi ko tabo ja-ja, fari-fari ya bayyana, dole yă gabatar da kansa ga firist.

  5. Firist zai bincike shi, in kuma ya zama ya fi fatar jiki zurfi kuma gashinsa ya juya ya zama fari, firist ɗin zai furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu a inda ƙurjin yake.

  6. Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, ya tarar babu farin gashi a ciki, kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, sai firist ɗin ya kaɗaice shi har kwana bakwai.

  7. In yana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist zai furta shi marar tsarki; cuta mai yaɗuwa ce.

  8. Amma in tabon bai canja ba, bai kuma yaɗu ba, tabo ne kawai daga ƙurji, kuma firist zai furta shi tsarkakakke.

  9. “Sa’ad da wani yana da ƙuna a fatar jikinsa, wurin kuwa ya yi ja-ja, ko fari-fari, ko kuwa farin tabo ya bayyana a sabon miki na ƙunan,

  10. firist zai bincike tabon, idan kuma gashin a cikinsa ya juya ya zama fari, kuma ya yi zurfi fiye da fatar jikin, cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu daga ƙunan. Firist zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa.

  11. Amma in firist ɗin ya bincike shi bai kuwa ga wani farin gashi a wurin ba, in kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, to, firist ɗin zai kaɗaice shi na kwana bakwai.

  12. A rana ta bakwai ɗin firist zai bincike shi, in kuma cutar tana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist ɗin zai furta shi marar tsarki, cutar fatar jiki ce mai yaɗuwa.

  13. In kuma wurin bai canja ba, bai kuma yaɗu cikin fatar jikin ba amma ya bushe, kumburi ne daga ƙuna, firist ɗin kuwa zai furta shi tsarkakakke; tabo ne kawai daga ƙuna.

  14. “In namiji ko ta mace tana da miki a kai ko kuwa a gemu,

  15. firist zai bincike mikin, in ya yi zurfi fiye da fatar jiki, gashin ya zama rawaya, ya kuma zama siriri, firist zai furta wannan mutum marar tsarki; ƙaiƙayi ne, cuta mai yaɗuwa ce na kai ko na gemu.

  16. Amma in, sa’ad da firist ya bincika wannan irin mikin, bai yi zurfi fiye da fatar jiki ba kuma babu baƙin gashi a cikinsa, firist ɗin zai kaɗaice mutum mai fama da cutar, kwana bakwai.

  17. A rana ta bakwai ɗin firist zai bincika mikin in kuwa ƙaiƙayin bai bazu ba, ba rawayan gashi kuma a ciki, babu zurfin da yake fiye da fatar jiki,

  18. dole a yi masa aski, sai dai ba zai aske wurin cutar ba, kuma firist zai kaɗaice shi kwana bakwai.

  19. A rana ta bakwai firist zai bincike ƙaiƙayin, idan bai bazu a fatar jikin ba, bai kuma yi zurfin fiye da fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi tsarkakakke. Dole kuma yă wanke rigunansa, zai kuwa zama tsarkakakke.

  20. Amma in ƙaiƙayin ya yaɗu a cikin fatar jikin bayan aka furta shi tsarkakakke,

  21. firist ɗin zai bincike shi, in kuma ƙaiƙayin ya yaɗu a fatar jikin, firist ɗin ba ya bukatar neman ganin rawayan gashi; mutumin marar tsarki ne.

  22. In fa a ganinsa bai canja ba kuma baƙin gashi ya fito a cikinsa, ƙaiƙayin ya warke ke nan. Mutumin tsarkakakke ne, firist ɗin kuwa zai furta shi tsarkakakke.

  23. “Sa’ad da namiji ko ta mace tana da farare wurare a fatar jiki,

  24. firist ya bincika su, in kuma wuraren toka-toka ne, to, ƙurji marar lahani ne ya faso a fatar jikin; wannan mutum tsarkakakke.

  25. “Mutumin da ya rasa gashi kansa ya zama mai sanƙo ke nan, duk da haka mutumin tsattsarka ne.