Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests

407 ayoyi · 86 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci.

  2. Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.

  3. Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.

  4. Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”

  5. Dole a bar wutar da take bisa bagaden tă yi ta ci; kada tă mutu. Kowace safiya firist zai ƙara itacen wuta, yă shirya hadaya ta ƙonawa a bisa wutar yă kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a kansa.

  6. Dole a bar wutar tă ci gaba da ci a bisa bagade; kada tă mutu.

  7. Kowane da namiji cikin iyalin firistoci zai iya ci. Sai a tsattsarkan wuri ne za a ci; gama abu mafi tsarki ne.

  8. “ ‘Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ƙa’ida hanyar yinsu iri ɗaya ce. Su ɗin na firist da ya yi kafara da su ne.

  9. Firist da ya miƙa hadaya ta ƙonawa domin wani, zai iya ajiye fatar wa kansa.

  10. Kowace hadaya ta garin da aka toya a tanda, ko aka dafa a tukunya ko a kan kaskon tuya, na firist da ya miƙa ta ne,

  11. kuma kowace hadaya ta gari wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, ita ma, ta dukan ’ya’ya Haruna ne maza.

  12. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza.

  13. Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”

  14. Sa’an nan Musa ya kawo Haruna da ’ya’yansa maza gaba, ya kuma wanke su da ruwa.

  15. Sa’an nan ya kawo ’ya’yan Haruna maza, ya sa musu taguwoyi, ya ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da su, ya kuma sa musu huluna yadda Ubangiji ya umarce shi.

  16. Sa’an nan ya miƙa bijimi domin hadaya don zunubi, sai Haruna da ’ya’yansa suka ɗibiya hannuwansu a bijimin.

  17. Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa.

  18. Musa ya ɗebo dukan kitsen da yake kewaye da kayan ciki, da kuma wanda ya rufe hanta, da ƙodojin, da kuma kitsensu, ya kuma ƙone su a kan bagade.

  19. Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  20. Sa’an nan ya miƙa ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan rago.

  21. Sa’an nan Musa ya yanka ɗan ragon, ya kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagaden.

  22. Ya yanka ragon gunduwa-gunduwa ya ƙone kan, ya kuma ƙone gunduwa-gunduwan da kitsen.

  23. Ya wanke kayan cikin da ƙafafun a ruwa, ya kuma ƙone dukan ragon a bisa bagade kamar hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  24. Sai ya miƙa ɗayan ɗan ragon, ɗan ragon naɗin, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan ragon.

  25. Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama.