Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests

407 ayoyi · 86 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare.

  2. Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne?

  3. Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne.

  4. Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna.

  5. Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba.

  6. Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.

  7. Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.