Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priests

407 ayoyi · 86 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. zai umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar a zubar a wuri marar tsarki waje da birnin.

  2. Dole yă sa a kankare duka shafen bangon cikin gidan a kuma zuba kayan da aka kankare a wurin marar tsarki waje da birnin.

  3. Sai su ɗebi waɗansu duwatsu su sa a wuraren da suka ciccire waɗancan, su kuma ɗiba sabon laka su yi shafen gidan.

  4. “In cutar fatar jiki da take ta rigar ta sāke bayyana a gidan bayan an ciccire duwatsu aka kankare gidan aka kuma yi shafe,

  5. firist zai je ya bincika shi, in kuwa cutar ta bazu a gidan, to, muguwar cuta ce; gidan marar tsarki ne.

  6. Dole a rushe gidan, a fid da duwatsun, katakai da kuma dukan shafen daga birnin zuwa wuri marar tsarki.

  7. Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.

  8. “ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ”

  9. Zai sa toguwar lilin mai tsarki, tare da ɗan ciki na lilin; zai yi ɗamara da igiya kewaye da shi, yă kuma sa hular lilin. Waɗannan su ne riguna masu tsarki; saboda haka dole yă yi wanka kafin yă sa su.

  10. Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da firistoci, ’ya’yan Haruna maza, ka ce musu, ‘Kada firist yă ƙazantar da kansa saboda wani cikin mutanensa da suka mutu,

  11. sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko ’yarsa, ɗan’uwansa,

  12. ko ’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa.

  13. Kada yă ƙazantar da kansa saboda mutanen da suke da dangantakar da shi ta wurin aure, ta yin haka zai ƙazantar da kansa.

  14. “ ‘Kada firistoci su aske kansu ƙwal ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsage jikunansu.

  15. Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.

  16. “ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.

  17. “Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni.

  18. Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki;

  19. ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu,

  20. ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba.

  21. Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba.

  22. Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki;

  23. duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’ ”

  24. Ubangiji ya ce wa Musa,

  25. “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji.