Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ministers

201 ayoyi · 118 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.

  2. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”

  3. Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.

  4. Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.

  5. Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”

  6. Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi.

  7. Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.

  8. Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’

  9. Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.

  10. Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.

  11. Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  12. Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu.

  13. Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.

  14. Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.

  15. Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikinsunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,

  16. Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.

  17. Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.

  18. Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”

  19. Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga.

  20. “Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”

  21. Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”

  22. Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”

  23. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.

  24. Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”

  25. Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”