Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Faɗi mini, abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka!” Elisha ya amsa ya ce, “Bari in gāji ninki biyu na ruhunka.”

  2. Iliya ya ce, “Ka nemi abu mai wuya, amma in ka ga lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, zai zama naka, in ba haka ba, ba za ka samu ba ke nan.”

  3. Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa.

  4. Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage.

  5. Sai ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya koma ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun.

  6. Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye.

  7. Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa.

  8. Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu nemi nufin Ubangiji ta wurinsa?” Wani hafsan sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, wanda dā ya yi wa Iliya hidima.”

  9. Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.

  10. Amma yanzu, a kawo mini makaɗin garaya.” Yayinda makaɗin garayan yake kiɗa, ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha

  11. Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”

  12. Ta ce wa mijinta, “Na san cewa wannan mutum da kullum yake zuwa nan mai tsarki ne na Allah.

  13. Bari mu yi ɗan ɗaki a rufin gida mu kuma sa masa gado da tebur da kujera da kuma fitila. Saboda a duk lokacin da ya zo wurinmu, sai yă sauka a can.”

  14. Da ta isa wurin mutumin Allah a dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo don yă ture ta, amma mutumin Allah ya ce, “Ka bar ta! Tana cikin baƙin ciki ƙwarai, amma Ubangiji ya ɓoye mini, bai kuma faɗa mini me ya sa ba.”

  15. Sai Elisha ya koma Gilgal, a can kuwa ana yunwa a yankin. Yayinda ƙungiyar annabawa suke tattaunawa da shi, sai ya ce wa Gehazi bawansa, “Ka sa babban tukunya a wuta, ka yi wa mutanen nan fate.”

  16. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.”

  17. Sai Na’aman ya je wurin maigidansa ya faɗa masa abin da yarinyan nan daga Isra’ila ta faɗa.

  18. Sarkin Aram ya ce, “Ko ta ƙaƙa, ka tafi, zan aika da wasiƙa ga sarkin Isra’ila.” Sai Na’aman ya tashi, ɗauke da talenti goma na azurfa, shekel dubu shida na zinariya, da tufafi kashi goma.

  19. Wasiƙar da ya kai wa sarkin Isra’ila ta ce, “Da wannan wasiƙa ina aika Na’aman gare ka don ka warkar da kuturtarsa.”

  20. Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!”

  21. Da Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra’ila ya yayyage tufafinsa, sai ya aika masa da wannan saƙo, “Don me za ka yayyage tufafinka? Ka sa mutumin yă zo wurina, zai kuwa san cewa akwai annabi a Isra’ila.”

  22. Sai Na’aman da dukan masu hidimarsa suka koma wurin mutumin Allah. Na’aman ya tsaya a gaban mutumin Allah ya ce, “Yanzu na san cewa babu wani Allah a duk duniya sai a Isra’ila. Ina roƙonka ka karɓi kyauta daga hannun bawanka.”

  23. Annabin ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji wanda nake bauta masa yana a raye, ba zan karɓi kome ba.” Ko da yake Na’aman ya yi ta roƙonsa, amma ya ƙi.

  24. To, fa, sarkin Aram yana yaƙi da Isra’ila. Bayan ya tattauna da hafsoshinsa, sai ya ce, “Zan kafa sansanina a wurin kaza da kaza.”

  25. Sai mutumin Allah ya aika wa sarkin Isra’ila cewa, “Ka yi hankali da wuce wuri kaza, domin Arameyawa za su gangara can.”