Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba.

  2. Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.

  3. Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna.

  4. In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci. Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.

  5. To, game da baye-baye na ruhaniya, ’yan’uwa, ba na so ku kasance da rashin sani.

  6. Kun san cewa sa’ad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana.

  7. Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.

  8. Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne.

  9. Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne.

  10. Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.

  11. An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa.

  12. Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda.

  13. Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda.

  14. Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna.

  15. Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.

  16. Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi.

  17. Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko ’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha.

  18. To, ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa.

  19. Da ƙafa za tă ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba.

  20. Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba.

  21. Da a ce dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma a ce dukan jiki kunne ne, da me za a sansana?

  22. Tabbatacce, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama.

  23. Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?

  24. Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.

  25. Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!”