circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 11:6kusan 59 M.
In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta.
- 1 Korintiyawa 11:7kusan 59 M.
Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.
- 1 Korintiyawa 11:8kusan 59 M.
Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.
- 1 Korintiyawa 11:9kusan 59 M.
Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.
- 1 Korintiyawa 11:10kusan 59 M.
Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.
- 1 Korintiyawa 11:11kusan 59 M.
Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba.
- 1 Korintiyawa 11:12kusan 59 M.
Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.
- 1 Korintiyawa 11:13kusan 59 M.
Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe?
- 1 Korintiyawa 11:14kusan 59 M.
Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi,
- 1 Korintiyawa 11:15kusan 59 M.
amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne.
- 1 Korintiyawa 11:16kusan 59 M.
In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah.
- 1 Korintiyawa 11:17kusan 59 M.
Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce.
- 1 Korintiyawa 11:18kusan 59 M.
Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.
- 1 Korintiyawa 11:19kusan 59 M.
Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.
- 1 Korintiyawa 11:20kusan 59 M.
Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba,
- 1 Korintiyawa 11:21kusan 59 M.
gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu.
- 1 Korintiyawa 11:22kusan 59 M.
Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!
- 1 Korintiyawa 11:23kusan 59 M.
Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi,
- 1 Korintiyawa 11:24kusan 59 M.
bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.”
- 1 Korintiyawa 11:25kusan 59 M.
Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.”
- 1 Korintiyawa 11:26kusan 59 M.
Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.
- 1 Korintiyawa 11:27kusan 59 M.
Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan.
- 1 Korintiyawa 11:28kusan 59 M.
Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin.
- 1 Korintiyawa 11:29kusan 59 M.
Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne.
- 1 Korintiyawa 11:30kusan 59 M.
Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci.