Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ibraniyawa 1:1kusan 64 M.

    A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,

  2. Ibraniyawa 1:2kusan 64 M.

    amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya.

  3. Ibraniyawa 1:3kusan 64 M.

    Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.

  4. Ibraniyawa 1:4kusan 64 M.

    Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

  5. Ibraniyawa 1:5kusan 64 M.

    Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”?

  6. Ibraniyawa 1:6kusan 64 M.

    Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce, “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”

  7. Ibraniyawa 1:7kusan 64 M.

    Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce, “Ya mai da mala’ikunsa iska, bayinsa kuma harsunan wuta.”

  8. Ibraniyawa 1:8kusan 64 M.

    Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka.

  9. Ibraniyawa 1:9kusan 64 M.

    Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”

  10. Ibraniyawa 1:10kusan 64 M.

    Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.

  11. Ibraniyawa 1:11kusan 64 M.

    Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga.

  12. Ibraniyawa 1:12kusan 64 M.

    Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”

  13. Ibraniyawa 1:13kusan 64 M.

    Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”?

  14. Ibraniyawa 1:14kusan 64 M.

    Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

  15. Ibraniyawa 2:1kusan 64 M.

    Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce.

  16. Ibraniyawa 2:2kusan 64 M.

    Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace,

  17. Ibraniyawa 2:3kusan 64 M.

    yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi.

  18. Ibraniyawa 2:4kusan 64 M.

    Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.

  19. Ibraniyawa 2:5kusan 64 M.

    Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba.

  20. Ibraniyawa 2:6kusan 64 M.

    Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa, “Mene ne mutum, da kake tuna da shi, ɗan mutum da kake kula da shi?

  21. Ibraniyawa 2:7kusan 64 M.

    Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku; ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,

  22. Ibraniyawa 2:8kusan 64 M.

    ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba.

  23. Ibraniyawa 2:9kusan 64 M.

    Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.

  24. Ibraniyawa 2:10kusan 64 M.

    Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.

  25. Ibraniyawa 2:11kusan 64 M.

    Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa.