Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Kolossiyawa 1:1kusan 64 M.

    Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

  2. Kolossiyawa 1:2kusan 64 M.

    Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku.

  3. Kolossiyawa 1:3kusan 64 M.

    Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku.

  4. Kolossiyawa 1:4kusan 64 M.

    Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka.

  5. Kolossiyawa 1:5kusan 64 M.

    Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar

  6. Kolossiyawa 1:6kusan 64 M.

    da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta.

  7. Kolossiyawa 1:7kusan 64 M.

    Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu,

  8. Kolossiyawa 1:8kusan 64 M.

    wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.

  9. Kolossiyawa 1:9kusan 64 M.

    Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.

  10. Kolossiyawa 1:10kusan 64 M.

    Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.

  11. Kolossiyawa 1:11kusan 64 M.

    Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki

  12. Kolossiyawa 1:12kusan 64 M.

    kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske.

  13. Kolossiyawa 1:13kusan 64 M.

    Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna,

  14. Kolossiyawa 1:14kusan 64 M.

    wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

  15. Kolossiyawa 1:15kusan 64 M.

    Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta.

  16. Kolossiyawa 1:16kusan 64 M.

    Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.

  17. Kolossiyawa 1:17kusan 64 M.

    Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

  18. Kolossiyawa 1:18kusan 64 M.

    Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici.

  19. Kolossiyawa 1:19kusan 64 M.

    Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi,

  20. Kolossiyawa 1:20kusan 64 M.

    ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

  21. Kolossiyawa 1:21kusan 64 M.

    A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.

  22. Kolossiyawa 1:22kusan 64 M.

    Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.

  23. Kolossiyawa 1:23kusan 64 M.

    Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.

  24. Kolossiyawa 1:24kusan 64 M.

    Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.

  25. Kolossiyawa 1:25kusan 64 M.

    Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai.