- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Korintiyawa 1:1kusan 60 M.
Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.
- 2 Korintiyawa 1:2kusan 60 M.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
- 2 Korintiyawa 1:3kusan 60 M.
Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya,
- 2 Korintiyawa 1:4kusan 60 M.
wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.
- 2 Korintiyawa 1:5kusan 60 M.
Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.
- 2 Korintiyawa 1:6kusan 60 M.
In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha.
- 2 Korintiyawa 1:7kusan 60 M.
Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
- 2 Korintiyawa 1:8kusan 60 M.
’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.
- 2 Korintiyawa 1:9kusan 60 M.
Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu.
- 2 Korintiyawa 1:10kusan 60 M.
Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,
- 2 Korintiyawa 1:11kusan 60 M.
yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.
- 2 Korintiyawa 1:12kusan 60 M.
Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.
- 2 Korintiyawa 1:13kusan 60 M.
Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa,
- 2 Korintiyawa 1:14kusan 60 M.
kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.
- 2 Korintiyawa 1:15kusan 60 M.
Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.
- 2 Korintiyawa 1:16kusan 60 M.
Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya.
- 2 Korintiyawa 1:17kusan 60 M.
Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?
- 2 Korintiyawa 1:18kusan 60 M.
Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce.
- 2 Korintiyawa 1:19kusan 60 M.
Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.
- 2 Korintiyawa 1:20kusan 60 M.
Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.
- 2 Korintiyawa 1:21kusan 60 M.
Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,
- 2 Korintiyawa 1:22kusan 60 M.
ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.
- 2 Korintiyawa 1:23kusan 60 M.
Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba.
- 2 Korintiyawa 1:24kusan 60 M.
Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.
- 2 Korintiyawa 2:1kusan 60 M.
Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba.