Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci.

  2. Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Sa’an nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu,

  3. gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani,

  4. don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna.

  5. In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.

  6. To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.

  7. A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.

  8. Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki?

  9. Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara?

  10. Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma. Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.

  11. In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai.

  12. In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.

  13. In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

  14. Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai.

  15. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

  16. Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya.

  17. Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

  18. Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

  19. Gama saninmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne.

  20. Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe.

  21. Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata.

  22. Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.

  23. Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

  24. Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci.

  25. Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.