- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 14:3kusan 59 M.
Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya.
- 1 Korintiyawa 14:4kusan 59 M.
Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina.
- 1 Korintiyawa 14:5kusan 59 M.
Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.
- 1 Korintiyawa 14:6kusan 59 M.
To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba?
- 1 Korintiyawa 14:7kusan 59 M.
Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?
- 1 Korintiyawa 14:8kusan 59 M.
Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?
- 1 Korintiyawa 14:9kusan 59 M.
Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai.
- 1 Korintiyawa 14:10kusan 59 M.
Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana.
- 1 Korintiyawa 14:11kusan 59 M.
To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni.
- 1 Korintiyawa 14:12kusan 59 M.
Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.
- 1 Korintiyawa 14:13kusan 59 M.
Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara.
- 1 Korintiyawa 14:14kusan 59 M.
Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba.
- 1 Korintiyawa 14:15kusan 59 M.
To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
- 1 Korintiyawa 14:16kusan 59 M.
A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?
- 1 Korintiyawa 14:17kusan 59 M.
Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
- 1 Korintiyawa 14:18kusan 59 M.
Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.
- 1 Korintiyawa 14:19kusan 59 M.
Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.
- 1 Korintiyawa 14:20kusan 59 M.
’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.
- 1 Korintiyawa 14:21kusan 59 M.
A cikin Doka yana a rubuce cewa, “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji.
- 1 Korintiyawa 14:22kusan 59 M.
Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba.
- 1 Korintiyawa 14:23kusan 59 M.
Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba?
- 1 Korintiyawa 14:24kusan 59 M.
Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi,
- 1 Korintiyawa 14:25kusan 59 M.
asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”
- 1 Korintiyawa 14:26kusan 59 M.
Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya.
- 1 Korintiyawa 14:27kusan 59 M.
In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara.