- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 10:14kusan 59 M.
Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka.
- 1 Korintiyawa 10:15kusan 59 M.
Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.
- 1 Korintiyawa 10:16kusan 59 M.
Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba?
- 1 Korintiyawa 10:17kusan 59 M.
Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.
- 1 Korintiyawa 10:18kusan 59 M.
Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba?
- 1 Korintiyawa 10:19kusan 59 M.
To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu?
- 1 Korintiyawa 10:20kusan 59 M.
A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu.
- 1 Korintiyawa 10:21kusan 59 M.
Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu.
- 1 Korintiyawa 10:22kusan 59 M.
Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?
- 1 Korintiyawa 10:23kusan 59 M.
“Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa.
- 1 Korintiyawa 10:24kusan 59 M.
Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma.
- 1 Korintiyawa 10:25kusan 59 M.
Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito,
- 1 Korintiyawa 10:26kusan 59 M.
gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”
- 1 Korintiyawa 10:27kusan 59 M.
In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito.
- 1 Korintiyawa 10:28kusan 59 M.
Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi
- 1 Korintiyawa 10:29kusan 59 M.
ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina?
- 1 Korintiyawa 10:30kusan 59 M.
In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
- 1 Korintiyawa 10:31kusan 59 M.
Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
- 1 Korintiyawa 10:32kusan 59 M.
Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah
- 1 Korintiyawa 10:33kusan 59 M.
kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.
- 1 Korintiyawa 11:1kusan 59 M.
Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.
- 1 Korintiyawa 11:2kusan 59 M.
Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku.
- 1 Korintiyawa 11:3kusan 59 M.
To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.
- 1 Korintiyawa 11:4kusan 59 M.
Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa.
- 1 Korintiyawa 11:5kusan 59 M.
Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan.