- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 8:4kusan 59 M.
To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.”
- 1 Korintiyawa 8:5kusan 59 M.
Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa),
- 1 Korintiyawa 8:6kusan 59 M.
duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.
- 1 Korintiyawa 8:7kusan 59 M.
Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu.
- 1 Korintiyawa 8:8kusan 59 M.
Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.
- 1 Korintiyawa 8:9kusan 59 M.
Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi.
- 1 Korintiyawa 8:10kusan 59 M.
Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba?
- 1 Korintiyawa 8:11kusan 59 M.
Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka.
- 1 Korintiyawa 8:12kusan 59 M.
Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan.
- 1 Korintiyawa 8:13kusan 59 M.
Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.
- 1 Korintiyawa 9:1kusan 59 M.
Ba ni da ’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba?
- 1 Korintiyawa 9:2kusan 59 M.
Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.
- 1 Korintiyawa 9:3kusan 59 M.
Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina.
- 1 Korintiyawa 9:4kusan 59 M.
Ba mu da ’yancin ci da sha ne?
- 1 Korintiyawa 9:5kusan 59 M.
Ba mu da ’yancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da ’yan’uwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi?
- 1 Korintiyawa 9:6kusan 59 M.
Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da ’yanci a ɗauke mana aikin ci da kai?
- 1 Korintiyawa 9:7kusan 59 M.
Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa?
- 1 Korintiyawa 9:8kusan 59 M.
Ina faɗin wannan bisa ga ra’ayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba tă faɗa haka ba?
- 1 Korintiyawa 9:9kusan 59 M.
Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka?
- 1 Korintiyawa 9:10kusan 59 M.
Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin.
- 1 Korintiyawa 9:11kusan 59 M.
In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba?
- 1 Korintiyawa 9:12kusan 59 M.
In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan ’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.
- 1 Korintiyawa 9:13kusan 59 M.
Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne?
- 1 Korintiyawa 9:14kusan 59 M.
Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar.
- 1 Korintiyawa 9:15kusan 59 M.
Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan ’yancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yă hana ni wannan abin taƙama.