- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 7:19kusan 59 M.
Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu.
- 1 Korintiyawa 7:20kusan 59 M.
Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.
- 1 Korintiyawa 7:21kusan 59 M.
Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama.
- 1 Korintiyawa 7:22kusan 59 M.
Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi.
- 1 Korintiyawa 7:23kusan 59 M.
Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane.
- 1 Korintiyawa 7:24kusan 59 M.
’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.
- 1 Korintiyawa 7:25kusan 59 M.
To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji.
- 1 Korintiyawa 7:26kusan 59 M.
Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke.
- 1 Korintiyawa 7:27kusan 59 M.
In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure.
- 1 Korintiyawa 7:28kusan 59 M.
Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.
- 1 Korintiyawa 7:29kusan 59 M.
’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;
- 1 Korintiyawa 7:30kusan 59 M.
waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne;
- 1 Korintiyawa 7:31kusan 59 M.
masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.
- 1 Korintiyawa 7:32kusan 59 M.
Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji.
- 1 Korintiyawa 7:33kusan 59 M.
Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa
- 1 Korintiyawa 7:34kusan 59 M.
hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta.
- 1 Korintiyawa 7:35kusan 59 M.
Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.
- 1 Korintiyawa 7:36kusan 59 M.
In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.
- 1 Korintiyawa 7:37kusan 59 M.
Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace.
- 1 Korintiyawa 7:38kusan 59 M.
Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.
- 1 Korintiyawa 7:39kusan 59 M.
Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji.
- 1 Korintiyawa 7:40kusan 59 M.
A nawa ra’ayi, za tă fi jin daɗi in ta zauna haka, a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.
- 1 Korintiyawa 8:1kusan 59 M.
To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.
- 1 Korintiyawa 8:2kusan 59 M.
Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba.
- 1 Korintiyawa 8:3kusan 59 M.
Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.