- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 9:16kusan 59 M.
Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba!
- 1 Korintiyawa 9:17kusan 59 M.
In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne.
- 1 Korintiyawa 9:18kusan 59 M.
To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba.
- 1 Korintiyawa 9:19kusan 59 M.
Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa.
- 1 Korintiyawa 9:20kusan 59 M.
Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka.
- 1 Korintiyawa 9:21kusan 59 M.
Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar.
- 1 Korintiyawa 9:22kusan 59 M.
Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.
- 1 Korintiyawa 9:23kusan 59 M.
Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
- 1 Korintiyawa 9:24kusan 59 M.
Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada.
- 1 Korintiyawa 9:25kusan 59 M.
Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama.
- 1 Korintiyawa 9:26kusan 59 M.
To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba.
- 1 Korintiyawa 9:27kusan 59 M.
A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.
- 1 Korintiyawa 10:1kusan 59 M.
Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku.
- 1 Korintiyawa 10:2kusan 59 M.
An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku.
- 1 Korintiyawa 10:3kusan 59 M.
Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda
- 1 Korintiyawa 10:4kusan 59 M.
suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne.
- 1 Korintiyawa 10:5kusan 59 M.
Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.
- 1 Korintiyawa 10:6kusan 59 M.
To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
- 1 Korintiyawa 10:7kusan 59 M.
Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”
- 1 Korintiyawa 10:8kusan 59 M.
Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu.
- 1 Korintiyawa 10:9kusan 59 M.
Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su.
- 1 Korintiyawa 10:10kusan 59 M.
Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su.
- 1 Korintiyawa 10:11kusan 59 M.
Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.
- 1 Korintiyawa 10:12kusan 59 M.
Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!
- 1 Korintiyawa 10:13kusan 59 M.
Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.