Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ox

111 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi.

  2. ’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma ’ya’yan dabbobinku, wato, ’ya’yan shanu da ’yan tumakinku.

  3. Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”

  4. Bayan Ehud, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya karkashe Filistiyawa ɗari shida da sandar korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra’ila.

  5. Kafin rana ta fāɗi a rana ta bakwai mutane garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaki? Me ya fi zaki ƙarfi?” Samson ya ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, da ba za ku san amsar kacici-kacici ba.”

  6. “Yanzu fa ku shirya sabon keken shanu da shanu biyu masu ba wa ’ya’yansu nono, waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba. Ku daure keken shanu wa shanun, amma ku tsare ’yan maruƙansu a gida.

  7. Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.

  8. Amma Sama’ila ya ce, “Ashe, waɗannan ba kukan tumaki ke nan nake ji a kunnena ba? Wane kuka shanu ke nan nake ji?”

  9. A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu.

  10. Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.”

  11. Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa.

  12. Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,

  13. Kwanon ya tsaya a kan siffofin bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar arewa, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, sa’an nan uku suna fuskantar gabas. Kwanon da ya kira Teku ya zauna a kansu, gindin siffofin bijimai goma sha biyun nan suna wajen tsakiya.

  14. Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha.

  15. Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa.

  16. Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.

  17. Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari.

  18. Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.

  19. Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi.

  20. yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.

  21. sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa,

  22. Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?

  23. Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari.

  24. Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.

  25. “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.