Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ox: Food

3 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Food

  1. Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,

  2. Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa.

  3. Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.